Quran Apps in many lanuages:

Surah Al-Ahqaf Ayahs #14 Translated in Hausa

قُلْ أَرَأَيْتُمْ إِنْ كَانَ مِنْ عِنْدِ اللَّهِ وَكَفَرْتُمْ بِهِ وَشَهِدَ شَاهِدٌ مِنْ بَنِي إِسْرَائِيلَ عَلَىٰ مِثْلِهِ فَآمَنَ وَاسْتَكْبَرْتُمْ ۖ إِنَّ اللَّهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ
Ka ce: "Shin, kun gani, idan (Alƙur'ãni) ya kasance daga wurin Allah yake, kuma kuka kãfirta da shi, kuma wani mai shaida daga Banĩ Isrã'ĩla ya bãyar da shaida a kan kwatankwacinsa, sa'an nan ya yi ĩmãni, kuma kuka kangare? Lalle Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai."
وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لِلَّذِينَ آمَنُوا لَوْ كَانَ خَيْرًا مَا سَبَقُونَا إِلَيْهِ ۚ وَإِذْ لَمْ يَهْتَدُوا بِهِ فَسَيَقُولُونَ هَٰذَا إِفْكٌ قَدِيمٌ
Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni: "Da (Alƙur'ãni) ya kasance, wani alhẽri ne," dã ba su riga muzuwa gare shi ba. Kuma tun da ba su shiryu game da shĩ ba, to, zã su ce, "Wannan ƙiren ƙarya ne daɗaɗɗe."
وَمِنْ قَبْلِهِ كِتَابُ مُوسَىٰ إِمَامًا وَرَحْمَةً ۚ وَهَٰذَا كِتَابٌ مُصَدِّقٌ لِسَانًا عَرَبِيًّا لِيُنْذِرَ الَّذِينَ ظَلَمُوا وَبُشْرَىٰ لِلْمُحْسِنِينَ
Alhãli kuwa a gabãninsa akwai littãfin Mũsã, wanda ya kasance abin kõyi, kuma rahama. Kuma wannan (Alƙur'ãni) littafi ne mai gaskatãwa (ga littafin Mũsã), a harshe na Larabci dõmin ya gargaɗi waɗanda suka yi zãlunci, kuma ya zama bushãra ga mãsu kyautatãwa.
إِنَّ الَّذِينَ قَالُوا رَبُّنَا اللَّهُ ثُمَّ اسْتَقَامُوا فَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ
Lalle ne waɗanda suka ce: "Ubangijinmu Allah ne," sa'an nan suka daidaitu, to, bãbu wani tsõro a kansu, kuma bã zã su yi baƙin ciki ba.
أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ الْجَنَّةِ خَالِدِينَ فِيهَا جَزَاءً بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Waɗannan 'yan Aljanna ne, sunã madawwama a cikinta, a kan sakamako ga abin da suka kasance sunã aikatãwa.

Choose other languages: