Quran Apps in many lanuages:

Surah Al-Anaam Ayahs #133 Translated in Hausa

وَكَذَٰلِكَ نُوَلِّي بَعْضَ الظَّالِمِينَ بَعْضًا بِمَا كَانُوا يَكْسِبُونَ
Kuma kamar wancan ne Muke jiɓintar da sãshen azzãlumai ga sãshe, sabõda abin da suka kasance sunã tãrãwa.
يَا مَعْشَرَ الْجِنِّ وَالْإِنْسِ أَلَمْ يَأْتِكُمْ رُسُلٌ مِنْكُمْ يَقُصُّونَ عَلَيْكُمْ آيَاتِي وَيُنْذِرُونَكُمْ لِقَاءَ يَوْمِكُمْ هَٰذَا ۚ قَالُوا شَهِدْنَا عَلَىٰ أَنْفُسِنَا ۖ وَغَرَّتْهُمُ الْحَيَاةُ الدُّنْيَا وَشَهِدُوا عَلَىٰ أَنْفُسِهِمْ أَنَّهُمْ كَانُوا كَافِرِينَ
Yã jama'ar aljannu da mutãne! Shin, manzanni daga gare ku ba su jẽ muku ba sunã lãbarta ãyõyiNa a kanku, kuma sunã yi muku gargaɗin haɗuwa da wannan yini nãku? Suka ce: "Mun yi shaida a kan kãwunanmu." Kuma rãyuwar dũniya tã rũɗẽ su. Kuma suka yi shaida a kan kãwunansu cẽwa lalle ne sũ, sun kasance kãfirai.
ذَٰلِكَ أَنْ لَمْ يَكُنْ رَبُّكَ مُهْلِكَ الْقُرَىٰ بِظُلْمٍ وَأَهْلُهَا غَافِلُونَ
Wanan kuwa sabõda Ubangijinka bai kasance Mai halaka alƙaryõyi sabõda wani zãlunci ba ne, alhãli kuwa mutãnensu sunã jãhilai.
وَلِكُلٍّ دَرَجَاتٌ مِمَّا عَمِلُوا ۚ وَمَا رَبُّكَ بِغَافِلٍ عَمَّا يَعْمَلُونَ
Kuma ga kõwanne, akwai darajõji daga abin da suka aikata. Kuma Ubangijinka bai zama mai shagala ba daga abin da suke aikatãwa.
وَرَبُّكَ الْغَنِيُّ ذُو الرَّحْمَةِ ۚ إِنْ يَشَأْ يُذْهِبْكُمْ وَيَسْتَخْلِفْ مِنْ بَعْدِكُمْ مَا يَشَاءُ كَمَا أَنْشَأَكُمْ مِنْ ذُرِّيَّةِ قَوْمٍ آخَرِينَ
Kuma Ubangijinika Wadãtacce ne Ma'abũcin rahama. Idan Yã so zai tafi da ku, kuma Ya musanya daga bãyanku, abin da Yake so, kamar yadda Ya ƙãga halittarku daga zũriyar wasu mutãne na dabam.

Choose other languages: