Quran Apps in many lanuages:

Surah Al-Hadid Ayahs #15 Translated in Hausa

مَنْ ذَا الَّذِي يُقْرِضُ اللَّهَ قَرْضًا حَسَنًا فَيُضَاعِفَهُ لَهُ وَلَهُ أَجْرٌ كَرِيمٌ
Wãne ne wanda zai ranta wa Allah rance mai kyau dõmin Allah Ya ninka masa shi (a dũniya) kuma Yanã da wani sakamako na karimci (a Lãhira)?
يَوْمَ تَرَى الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ يَسْعَىٰ نُورُهُمْ بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَبِأَيْمَانِهِمْ بُشْرَاكُمُ الْيَوْمَ جَنَّاتٌ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ
Rãnar da zã ka ga mũminai maza da mũminai mãtã haskensu nã tafiya a gaba gare su, da kuma dãma gare su. (Anã ce musu) "Bushãrarku a yau, ita ce gidajen Aljanna." Ruwa na gudãna daga ƙarƙashinsu sunã mãsu dawwama a cikinsu. Wannan, shĩ ne babban rabo mai girma.
يَوْمَ يَقُولُ الْمُنَافِقُونَ وَالْمُنَافِقَاتُ لِلَّذِينَ آمَنُوا انْظُرُونَا نَقْتَبِسْ مِنْ نُورِكُمْ قِيلَ ارْجِعُوا وَرَاءَكُمْ فَالْتَمِسُوا نُورًا فَضُرِبَ بَيْنَهُمْ بِسُورٍ لَهُ بَابٌ بَاطِنُهُ فِيهِ الرَّحْمَةُ وَظَاهِرُهُ مِنْ قِبَلِهِ الْعَذَابُ
Rãnar da munafikai maza da munãfikai mãtã ke cẽwa waɗanda suka yi ĩmãni: "Ku dũbẽ mu, mu yi makãmashi daga haskenku!" A ce (musu): "Ku kõma a bãyanku, dõmin ku nẽmo wani haske." Sai a danne a tsakãninsu da wani gãru yanã da wani ƙyaure, a cikinsa nan rahama take, kuma a bãyansa daga wajensa azaba take.
يُنَادُونَهُمْ أَلَمْ نَكُنْ مَعَكُمْ ۖ قَالُوا بَلَىٰ وَلَٰكِنَّكُمْ فَتَنْتُمْ أَنْفُسَكُمْ وَتَرَبَّصْتُمْ وَارْتَبْتُمْ وَغَرَّتْكُمُ الْأَمَانِيُّ حَتَّىٰ جَاءَ أَمْرُ اللَّهِ وَغَرَّكُمْ بِاللَّهِ الْغَرُورُ
Sunã kiran su, "Ashe, bã tãre muke da ku ba?" Su ce: "Ĩ, amma kũ, kun fitini kanku, kuma kun yi jiran wata masĩfa, kuma kunyi shakka, kuma waɗansu gũrace-gũrace sun rũɗe ku, har umurnin Allah ya jẽ muku, kumamarũɗi ya rũɗe ku game da Allah."
فَالْيَوْمَ لَا يُؤْخَذُ مِنْكُمْ فِدْيَةٌ وَلَا مِنَ الَّذِينَ كَفَرُوا ۚ مَأْوَاكُمُ النَّارُ ۖ هِيَ مَوْلَاكُمْ ۖ وَبِئْسَ الْمَصِيرُ
"To, a yau bã zã a karɓi fansa daga gare ku ba. Kuma bã zã a karɓa daga waɗanda suka kãfirta ba. Makõmarku wutã ce, ita ce mai dacẽwa da ku, kuma makõmarku ɗin nan tã mũnana."

Choose other languages: